Hamshakan Masu Kudin Nijeriya Sun Boye Dala Biliyan 20 —CBN

0
922

Rabo Haladu, Daga Kaduna.
SHUGABAN babban bankin Nijeriya, Mista Godwin Emefiele, ya ce wasu hamshakan masu

kudin kasar sun boye kimanin Dala Biliyan 20 a bankunan kasar daban-daban.

Mista Emefiele ya ce boye kudaden ne ya janyo matsalar karancin dalar Amurka da ake
fuskanta a Nijeriya, lamarin da ya sa darajar Naira ke ci gaba da faduwa.

Gwamnatin ta kayyade Dala daya a kan Naira 197, sai dai a kasuwar musayar
kudaden waje ta bayan-fage ana sayar da kowacce Dala daya a kan fiye da Naira 325.

Shugaban babban bankin ya ce wasu \’yan kasar masu muguwar aniya ce ke boye Dalar da
zummar ci gaba da samun kudi ta mummunar hanya. Karancin Dalar dai ya sanya tattalin arzikin
Nijeriya ya fada cikin mawuyacin hali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here