Kwastan Sun Kashe Matashi A Kan Buhun Shinkafa Biyu

0
1236

Daga Usman Nasidi

WANI magidanci mai suna Malam Lawwali Hamidu ya zargi ma’aikatan Hukumar Kwastan a ke aiki a kan iyakar Najeriya da Nijar a karamar Hukumar Illela da ke Jihar Sakkwato da kashe dansa a kan buhun shinkafa biyu.

Malam Lawwali Hamidu ya ce a ranr Lahadin da ta gabata ne jami’an na Kwastam da ke kan hanyar iyakar suka harbe dansa matashi mai kimanin shekara 25 mai suna Shu’aibu Lawwali da ke tuka mota wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.

Malam Lawwali Hamidu a gidansa da ke Unguwar ’Yan Alewa a karamar Hukumar Gwadabawa, ya shaida cewa “Shu’aibu ne dana na uku daga cikin ’ya’yana 20 kuma yana kyautata min sosai ina jin sanyinsa, na samu labarin rasuwarsa ta bakin ’yan uwansa, wadanda suka zo suka fada min cewa ma’aikatan Kwastan sun harbi dana a kusa da wurin bincike na sojoji amma ’yan sanda sun tafi da shi Sakkwato don gudanar da bincike.

Bayan samun wannan labarin ne da awowi kadan sai ga ’yan sandan sun zo nan gidana da gawar marigayin a daure da kafa da hannu duk kansa ya baci ba kyan gani.”

Malam Lawwali ya kara da cewa “Sun kashe min dana kan buhu biyu na shinkafa da ya dauko daga Illela, wannan ya kara tabbatar min da cewa tsohuwar azazzar da ke tsakaninsu ne ya sanya suka harbe shi a wulakance domin a wasu lokuta da suka gabata da suka kama shi suka mika shi ga sojoji aka yi masa dukan tsiya sai da ya suma aka kai shi asibiti daga baya ya farfado ashe suna biye da ransa.

Don haka ina kira ga gwamnati da hukumomin kasar nan su kwato min hakkin dana da aka yi wa kisan gilla ba wani laifi, ina wanda ya kashe min dana shi ma a kashe shi kamar yadda ya yi wannan zalunci da bata wa hukumarsa da kasa baki daya suna.”

Wakilinmu ya ji ta bakin Nura Bello Gwadabawa wanda ke tafiya tare da marigayin har zuwa lokacin da aka harbe shi, inda ya ce, “A lokacin da muka fito daga Illela muka wuce wadannan jami’an na Kwastan sai suka biyo mu suka same mu a wurin binciken sojoji na kusa ga garin Gwadabawa suka umarcemu da mu koma.

Ya ce , a nan take na ce ba za mu koma ba a tsaya nan dai a yi sulhu kawai sai daya ya harbe mana taya ta gaba a gefen direba daga nan na fito da babbar murya na ce don Allah jama’a a taimake mu, ganin ni kadai ne a wurin kada su zalunce mu. Ana haka babbansu ya fito waje kai-tsaye ya tafi wurin direba ya daga bindiga sama daidai fuskar direban sauran jami’an suna bayansa don su shida ne suna fadin “Oga kada ka harbe shi,” har sau uku amma sai ya harbe shi a ido har harsashi ya fita ta bayan kansa, sai marigayin ya saukar da kafarsa daya da gilashin mota.”

Ya kara da cewa Daga nan sai suka wuce abinsu. Bayan sun tafi ne sojoji suka zo kusa da mu daya na ganin gawar sai ya fashe da kuka daga nan suka dauko motar suka bi Kwastan din har zuwa kauyen Gaidau da ke karamar Hukumar Illela amma ba su gansu ba, a tare da ni ake tafiya sai muka dawo ashe cikin daji suka shige suka boye.

A cewarsa, \’\’Ba wata sa-in-sa da ta shiga tsakaninsu da marigayin kuma shi kadai suka biyo don a cikin jerin gwanon motoci yake kusan 300 wadanda za su je yakin neman zaben kananan hukumomi da za a yi a Jihar Sakkawato ga ba wani tashin hankali don sun duba motarmu buhun shinkafa biyu suka samu a cikin motar, mu ba ’yan sumoga ba ne fasinjan kauyuka muke dauka.

Ya ce mun baro Illela ne don an kira mu za mu dauki masu zuwa kamfen din siyasa. Dama suna da takaicinsa domin sun taba tare shi ya gaya musu shi ba ya sumoga ashe maganar ta yi musu zafi suka rike shi a zuciya yanzu kuma suka harbe shi.

Babban Jami’in Hukumar Kwastan mai kula da Sakkwato da Kebbi da Zamfara Malam Sani Madugu ya yi magana da manema labarai kan wannan lamarin inda ya nuna kisan a matsayin
wanda za a yi da-na-sanin aiwatar da shi don ba wanda ya umarci jami’in Kwastan ya harbi wani balle ya kashe shi.

Ya ce sun mika dukkan jami’an da ake zargi ga rundunar ’yan sanda ta jihar don gudanar da bincike. Ya ce sun san akwai sabani tsakanin ’yan sumoga da jami’ansu amma ba shi zai sanya a harbi mutum ba.

A cewarsa, babu wata doka da ta ce jami’in Kwastan ya harbi dan sumoga sai in shi ya kawo masa hari don ya kare kansa, don haka duk wanda aka samu da laifi za a kai shi kotu domin ta hukunta shi, muna jiran ’yan sanda su kammala bincikensu, kuma za mu yi kokarin hada kai da sarakunan gargajiya da ke wuraren don samar da zaman lafiya ga jami’anmu,” inji Sani Madugu

A binciken da aka gudanar ya nuna cewa wannan shi ne karo na uku da jami’an Kwastan suke sanadiyyar rasa rayukan direbobin mota a kan hanyar, sai dai wannan ne mafi muni da ya faru inda mutanen gari suka kone tantin jami’an suka tarwatsa su kuma har zuwa hada wannan rahoton ba su koma wurin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here