Rabo Haladu, Daga Kaduna.
MINISTA a ma\’aikatar man fetur Dokta Ibe Kachikwu, ya ce za a rarraba kamfanin NNPC zuwa kamfanoni 30 wadanda za su dinga samar da riba.
Kamfanonin za su sami manajojin daraktoci a makonni masu zuwa, a wani bangare na gyare-
gyare da ake yi wa kamfanin man na NNPC.
Dokta Kachikwu ya yi wannan jawabin ne a wurin taron laccar mai da aka yi a Abuja.
Ministan ya kara da cewar kamfanin NNPC ya farfado daga asarar naira biliyan 160 zuwa
naira biliyan uku a watan Janairun shekarar 2016, inda ya kara da cewar ana sa ran zuwa
karshen shekara, kamfanin zai fara samun riba.
Mista kachikwu ya ce a karon farko, za su rarraba bangarori daban-daban na kamfanin
NNPC zuwa kamfanoni 30 masu zaman kansu da manajojin daraktoci.
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana mayar da hanakali ne kan ci gaban albarkatun iskar gas na kasa, domin bunkasa kudaden shigar kasar a wani bangare na manufar gwamnatin tarayya na kaucewa daga dogaro da mai domin samun kudaden shiga
\”Sharhin Masana\”
Ba tun yau ba wasu masana ke kiraye-kirayen a karkasa kamfanin na NNPC zuwa rukunoni
daban daban, musamman batun raba bangaren da ke sa ido kan yadda ake tafiyar da sashen
man fetur din, da kuma bangaren kasuwanci da zuba jari a bangaren na man fetur.
Sai dai a cewar ministan mai Ibe Kachukwu, karkasa kamfanin zai taimaka wajen inganta
yadda ake tafiyar da al\’amura a cikinsa.
Yayin da wasu masu sharhi a kan harkokin man fetur a kasar ke marhabin da wannan
sanarwar, wasu ko cewa suke, karkasa kamfanin zuwa kashi 30 ka iya sa wa a koma
gidan jiya, domin za a nada shugabanni 30 kenan, ana biyansu albashi da kuma ma\’aikatan
da za su taimaka musu, maimakon shugaba daya da ake da shi a yanzu.
Wasu kuma na ganin wannan ba shi ne lokacin da ya dace a dauki wannan matakin ba, domin farashin mai ya fadi kasa a kasuwannin duniya, hakan ya sa babu masu zuba jari sosai asashen.
An dai shafe shekaru da dama ana zargin cewa sashen man fetur din na Najeriya na cike da
cin hanci da rashawa, abinda ya sa kamfanin man ba ya samun riba sai dai faduwa.