Daga Usman Nasidi
Wani jaki ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 19 lokacin da ya jawo hadarin motoci kan hanyar Kano zuwa Maiduguri a gab da kauyen Zubo da ke tsakanin Azare da Jama’are a Jihar Bauchi.
Wasu motoci biyu na daukar fasinja, daya kirar Toyota bas (Homa) dauke da mutum 18 da Golf karama dauke da mutum hudu ne suka kara inda mutum 18 suka rasu nan take.
Wani da yake kusa da wurin da hadarin ya faru
da ya ki bayyana sunansa ya bayyana cewa, hadarin ya faru ne da misalin karfe 2:45 na ranar Asabar lokacin da jakin ya yi kokarin ketare hanya inda direban Golf din da ya taso daga Azare ya yi kokarin kauce wa jakin sai motar ta doki jakin ta kuma taho-mu- gama da bas din da ta taso daga Kano zuwaMaiduguri, inda bas din ta kama da wuta.
Ganau din ya kara da cewa, Golf din kuma ta rika juyawa a gefe guda, kuma nan take mutum 16 daga cikin basu din suka kone yayin da mutum biyu da ke cikin Golf din suka rasunan take, sauran biyun kuma da suka ji munanan raunuka aka kwashe su zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare, inda daga bisani daya daga cikinsu ya cika.
Shugaban Hukumar Kiyaye Hadurra a Shiyyar Azare, Malam Yusuf Sa’ad Yusuf Funtuwa ya tabbatar da faruwar hadarin, inda ya ce motocin biyu sun yi taho-mu-gama ne a kokarin kauce wa wani jaki da direban Golf din ya yi, kuma mutum 17 ne suka rasu amma wasu na asibitin Azare suna jinya.
Malam Yusuf Funtua ya ce, akwai bukatar direbobi su rika kula da yadda suke gudanar da tuki tare da guje wa gudun da ya wuce kima wanda ya ce galibi shi yake haifar da hadari.
Ya kuma gargadin direbobi su guje wa halayyar daukar fasinojin da suka wuce kima a motocinsu domin yin hakan ba ya da alfanu.