Mutum 1 Ya Mutu Motoci 9 Sun Salwanta

0
1237

IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna
SHUGABAN kungiyar direbobin Tanka ta kasa reshen Jihad Kaduna Kwamared Musa Ibrahim Dan Azumi,ya tabbatar wa da manema labarai salwantar ran wani direba daya da kuma asarar motocin Tanka guda 9 a wasu lokutan da suka gabata.

Kwamared Dan Azumi, ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin Kaduna.

Ya CE hakika a yankin Birnin Gwari an samu matsala inda aka budewa wani direba wuta ya mutu kuma wasu barayin mota yan fashion suka haifar da matsala a wata motar da ta dauko mai daga Legas zuwa garin Damaturu na Jihar Yobe aka tare motar aka karbe ta da bakin bindiga.

Amma kamar yadda shugaban Direbobin tankar ya bayyana an samu nasarar kame motar a can wajen Tafa bayan wani kokarin aiki tsakanin jami an tsaro da kuma direbobi yayan kungiyar.

Ya kuma CE yayan kungiyarsa suna samun matsala a yankin birnin Gwari da ya hadar da Buruku inda a wasu lokuta idan direbobi suka tsaya domin gyara mota idan ta lalace sai kawai yan fashion su bude masu wuta haka kawai.

Don haka suna kira ga gwamnati da sauran Jami an tsaro da su ci gaba da taimaka masu domin kawo karshen wannan matsalar.

A game da irin yadda dangantaka take tsakanin yayan kungiyar ya bayyana cewa lamarin abu ne mai armashi kwarai domin zaman lafiya a koda yaushe na kankama a tsakaninsu.

Ya kara da cewa hakan kuwa ya faru ne sakamakon irin yadda ya rungumi kowa ana tafiya tare ba bu wani bambanci ko kadan saboda haka ana tafiya uwa daya uba daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here