YA KASHE KANINSA YA KONA GAWAR

0
1415

Daga Usman Nasidi

Wani matashi mai suna Abdullahi Mati mai kimanin shekara 30 ya hada baki da abokinsa mai suna Mamman Garba a kauyen Gidan-Kara a karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa inda suka kashe kanensa mai suna Haruna Mati mai
kimanin shekara 28 a kan babur din da mahaifiyarsu ta saya musu domin su rika zuwa makaranta kuma suna yin acaba domin su samu dogaro da kansu.

Lokacin da aka gurfanar da Abdullahi a gaban wata kotun Majistare da ke Jihar Jigawa ya shaida wa alkalin kotun Majistare A’isha Ahmed babura cewa, ya yi kisan ne domin ya mallake babur din shi kadai da Allah Ya sa asirinsa bai tonu ba.

Da yake wa alkali karin bayani Mamman Garba ya ce ya taya Abdullahi Mati yayan Haruna wajen kashe shi ta hanyar makare shi da amfani da sanda da wukake har sai da suka tabbatar ya rasu.

Ya ce da suka tabbatar marigayin ya rasu ne sai suka sanya gawarsa a cikin wani rami suka banka mata wuta suka kone gawar suka binne shi.

Majistare A’isha Ahmed babura ta ingiza keyar wadanda ake tuhuma har sai ranar 21 ga watan Maris inda za a ci gaba da sauraren shari’ar.

Mahaifin matasan biyu wato Alhaji Mati ya roki kotun da ta zartar wa Abdullahi hukuncin kisa saboda sake shi yana iya zama barazana a wajensa domin ya yi ikirarin hallaka shi idan ya fito daga hannun hukuma.

Ita ma mahaifiyar matasan biyu Hajiya A’isha wadda aka fi sani da Ladi Mai kosai ta ce babu ita babu dan nata Abdullahi ko a Lahira, kuma ta roki kotu da ta yanke masa hukuncin kisa domin hakan ne zai sa hankalinsu ya kwanta.

Ladi Mai kosai ta ce ta sayi babur din ne domin amfanin su biyun, kuma ba ta taba tunanin Abdullahi yana da burin hallaka kanensa ba sai da hakan ta kasance, inda ta ce ta yi da-na- sanin yadda lamarin ya faru ta kuma gargadi iyaye su rika sanya idanu sosai a kan yadda ’ya’yansu suke tafiyar da rayuwarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here