AN TSINCI WANDA AKA FARKEWA CIKI

0
1104

DAGA USMAN NASIDI

A safiyar talatar da ta gabata ne aka tsinci wani mutum da aka farke wa ciki tare da wadansu ‘yan uwansa biyu da aka yi musu yankan rago a yashe a wani kwari da ke wani kauye mai suna Mahangi kusa da Karaukarau da ke makwabtaka da dajin Kudaru a karamar hukumar Giwa ta jahar Kaduna.

A binciken da aka yi a kauyen Mahangi inda aka tarar da jama’a sun taru suna ta mahawara a kan wadannan mutanen, duk da kasancewa wanda aka farke wa ciki bai mutu ba kuma yana iya Magana, amma ya kasa fadin sunansa da kuma sunan ‘yan uwansa wadanda aka yi wa yankan rago da kuma dalilin da ya sa aka aikata musu haka da kuma inda aka kwaso su aka kawo su nan.
Sai dai ya fadi inda suke da zama, inda ya ce suna zaune ne a gidan wani mai suna Malam Abdu da ke Unguwan Katafawa. Amma an yi ta kokari domin ya fadi dalilin da ya sa aka aikata masu wannan mugun abu ya ki fadi, sai dai fadi yake a dai kai shi asibiti. Kuma a jikinsa da na ‘yan uwansa da aka yanka akwai alamun robar karin ruwa, wanda ke nuna alamar an yi kokarin yi musu magani kafin a kawo su nan a watsar da su.
Wadanda wakilinmu ya tarar a wurin sun yi masa bayanin cewa, an tarar da wadanna mutane ne a yashe a wannan wurin kuma ba a san daga inda suke ba, ‘’sai dai muna zaton barayi ne, tun da ka ji shi wannan me sauran nunfashin ya ki fadin inda suke da kuma abin da ya sa aka yi musu haka, ka san ba su da gaskiya, tun da kowa ya san halin da wannan bangaren namu yake ciki na hallaka mutane tare da kwashe masu dukiya da kuma sace musu mutane ana garkuwa da su don samun kudin fansa, wanda hakan ya haifar da‘yan gari ke kokarin kare kansu, ta iya yiwuwa sun tafi ne domin yin mugun aiki dubunsu ta cika, su kuma wadanda suka aikata musu hakan suka kwaso su suka watsar da su a nan.’’
Binciken wakilinmu ya bayyana cewa mutanen wannan yakin sun dade suna fuskantar barazanar ‘yan fashi da makami da kuma sace masu iyalansu da ake yi ana garkuwa da su, wadansu har fyade ake wa matansu, wannan ya jawo al’ummomin da ke zaune a wadannan yankunan suke ta hijira suna barin yankunan don kare mutuncinsu da rayukansu.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna ASP Zubairu Abubakar domin jin ko an san wadannan mutane da kuma dalilin da ya sa aka yi musu wannan aikin, sai ya ce in ba shi lokaci zai kira, amma har zuwa buga wannan rahoton bai kira ba.

Shi kuma Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya AC Muhammadu Shehu, ya ce bayanin bai zo gabansa ba. Amma wani dan sanda da bai so a ambaci sunansa, ya ce shi wanda ma aka farke wa cikin ya mutu, kuma sun kwashe gawarwakin duka guda ukun sun kai su asibitin koyarwa na Jam’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here