Usman MB Nasidi
Wata yarinya mai suna Fatima Abdurrashid mai kimanin shekara 10 ta tsallake rijiya da baya sakamakon azabtar da ita da kishiyar mamanta ke yi bayan rasuwar mahaifiyarta inda yanzu haka take kwance a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya domin jinyar raunukan da ta yi mata.
Yariyar wanda suke zaune a gidan Alhaji Yahaya na Malam Mai Aljana a Unguwar Alkali a Zariya Jihar Kaduna, ta shaida cewa, “Bayan babana ya dauke mu ni da kanwata wadda ta rasu mai suna Narjis ya tafi da mu Gombe ya bar mu tare da matarsa, to bayan ya tafi sai ta fara azabtar da mu ta hanyar hana mu abinci.
Sai ta samu a wani daki da ke hade da bayi sai tasa mana ruwa a gora shi ne muke sha ni da kwanwata idan ruwan ya kare sai dai mu rika kuka mukan yi kwana uku ko hudu ba ta bude mu ba, ba ruwa ba abinci in ta bude mu kuma ta rika dukanmu tana kokona mu ko ta yayyanka mana jiki da reza Haka ta yi ta yi mana har rashin lafiya ya kama mu.”
Fatima ta ce ranar da babansu ya koma da ya gansu sai ya fashe da kuka shi ne ya kwashe su zuwa asibiti, kuma bayan an kwantar da su sai kanwarta Narjis ta rasu.
Tace “Bayan babana sun tafi da ita gida sai likitan ya fara yi min tambayoyi shi da wata mata ni kuma na fada masa duk abin da yake faruwa to daga nan sai ya sa wannan matan ta dauke ni ta tafi da ni ta aje ni a wajenta har lokacin da wasu mutane suka zo suka yi min tambayoyi kafin ’yan uwana su zo daga Zariya aka hada su da ni suka kawo ni nan.
Ta yanka min baki da reza ta kuma kokkona min bayana kuma kullum sai ta buge ni ta yayyanka jikina haka ta yi wa kwanwata tunda gidan mu kadai ne a ciki,” inji ta.
Wani likita da ya nemi a sakaye sunansa ya ce yarinyar ta samu lahani a hannu kuma akwai alamun raunin a kashin bayanta, kuma akwai yunwa a tare da ita sai dai za su dauki matakin da ya dace don duba lafiyarta kuma za ta warke ba da dadewa ba.
Shugaban Asibitin Farfesa Lawal Khalid ya ce bai san da maganar ba amma zai bincika kuma zai yi bayani.
Wakilinmu ya tuntubi kakar yarinyar wadda ta haifi mahaifiyar Fatima mai suna Sa’adatu, Hajiya Babuwa Mahmud ta ce bayan Sa’adatu ta rabu da mahaifin yaran saboda wasu dalilai na lullube karya da ya yi kafin a ba shi aurenta,
“Tana zaune da mu ita da ’ya’yanta tsawon shekara uku da rabi domin a lokacin ita karamar wato Narjis an haife ta ba dadewa har Allah Ya sa mahaifiyarsu ta rasu.
To kafin lokacin ya yi ta kokarin a ba shi yaran ba a ba shi ba, sai bayar rasuwar mahaifiyar da wata shida da suka zo taronsu na Shi’a a nan Zariya wata uku da suka wuce wanda suke tafiya da kafa din nan to a lokacin ne fa suka zo gidanmu tare da mutanensu suka ce dole ne a ba su ’ya’yansu Malam ya turo su domin su umarnin Malam suke bi. Idan ba a ba su ba, za su kaddamar da jihadi a gidan.
Muka ce mene ne na jihadi ai ’ya’yanka ne don haka muka shawarta aka dauki yaran aka ba shi har sun fara karatu a nan suka tafi da su kuma ba mu sake jin duriyarsu ba sai da wannan abin ya faru na rasuwar karamar tare da rashin lafiyar babbar da kuma irin kokarin da ma’aikatan asibiti suka yi da kuma masu kare hakkin kananan yara da yarinyar ta yi akalla wata daya a hannunsu kafin mu gano inda suke suka dauka suka ba mu bayan kula da lafiyarta.
Ta ce wannan ya nuna cewa matar babansu ita ta kashe Narjis kuma ta kara da cewa wadanda suka ba su jikarsu Fatima sun ce sun shigar da kara a can garin Gombe kuma za su neme su idan aka bukace su.
Inna lillahi WA inna ilaihi Raji’un. Allah wadaran mummnar akida ta Shi’a. Iyaye musamman maza mu kara kulawa akan ‘ya’yanmu musamman wadanda basu tare da mahaifiyarsu a gidan Uba.