An Yi Zaman Sulhu Tsakanin Kwankwaso da Ganduje.

    1
    2773

    Rabo Haladu Daga Kaduna

    Rahotanni na cewa ana yunkurin sulhunta
    gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje
    da kuma wanda ya gada Sanata Rabiu Musa
    Kwankwaso.
    Bayanai sun ce akwai yunkuri da ake yi a
    matakai da dama na ganin an dai-dai ta
    tsakanin bangarorin biyu ya yi nisa, kuma har ana fatan kwalliya zata biya kudin sabulu.
    Bayanai sun ce bangarori da dama a ciki da
    wajen jihar Kano sun damu da rikicin da ya barke tsakanin gwamna Ganduje da Sanata Kwankwaso, mutanen da aka sansu da aminci na siyasa shekaru da dama.
    Daga cikin wadan da suke yunkurin sasanta rikicin dai akwai gwamnonin shiyyar arewa maso yamma, da wasu dattijan jihar Kano, da kuma kwamitin da uwar jam\’iyyar APC ta kafa.
    Bayanan dai sun ce an yi nisa sosai wajen tattaunawar da ake yi da shugabannin guda biyu, kuma kowanne daga cikin su ya nuna amincewa da matakan da ake dauka na kawo karshen wannan sabani.
    Mai bawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje
    shawar na musamman a al\’amuran siyasa Alhaji Abdullahi Abbas ya tabbatar wa manema labarai cewa bangarori da dama sun zauna da gwamnan inda suka tattauna a kan bukatar a dakatar da rikicin a kuma sasanta da bangaren Sanata
    Kwankwaso.
    Alhaji Abdullahi Abbas ya ce a shirye suke a yi sulhu matukar za a ajiye komai a gurbin sa.
    Shi ma Dr. Adamu Yunusa Dan Gwani na
    bangaren tsohon gwamna Sanata Rabiu Musa
    Kwankwaso yace an zauna da tsohon gwamnan
    ba sau daya ba ba sau biyu ba, kuma a cewar
    sa dama su sun jima suna daukar duk matakan
    da za su kaucewa haifar da irin wannan rigima.
    Masana al\’amuran siyasa dai sun ce jama\’ar da
    ake mulka a Kano sune za su fi kowa cutuwa da wannan rikici da ake yi, haka kuma ita ma jam\’iyyar APC za ta iya samun mummunan koma baya a jihar matukar rikicin ya ki ci ya ki
    cinye wa.

    1 COMMENT

    1. Assalam ni badan jihar Kano bane ni Dan sokoto ne amma rikicin siyasar Kano yana damuna domin duk inda kaga rikicin irin wannan zai iya gurgunta jamiyar ka sai yan adawa su shigo suna fadar albarkacin bakinsu to Allah yasa adaidai ta amen amma ganduje kabi duniya ahankali domin kuwakayi butulci kadaina biyema giyar Mulkikazauna da abokin ka nasanku tare batun yauba Allah yasa mudace amen

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here