Wani Matashi Ya Kona Abokinsa

0
1221

DAGA USMAN NASIDI

Yanzu haka wani matashi mai suna Mubarak Abubakar na Unguwar Satatima a karamar Hukumar Birnin Kano a Jihar Kano yana can yana jinyar raunin da ya samu sakamkon kona shi da abokinsa ya yi da man fetur.

Lamarin ya faru ne a Unguwar Agadasawa kofar Maigishiri a lokacin da abokan biyu suke hira sai fetur ya zuba a jikin Mubarak inda abokinsa Hassan cikin wasa ya kyasta masa ashana wuta ta tash a jikin Mubarak ta kona masa ciki da hannuwa biyu.
Mubarak wanda ke kwance a Asibitin Murtala ya shaida cewa abokinsa Hassan ne ya kyasta masa ashana bayan fetur ya zuba masa a jiki.
Ya ce “Na fito daga gida sai na ga wani dan makwabtanmu da man fetur yana zubawa a motar gidansu, na ce don Allah ya sam min kadan zan sa a inji. Sai ya rage min kamar kwata na samu farar leda na juye a ciki. Sai abokina Hassan ya ce in ba shi mu sa a babur, Ni kuma
na ce masa zan yi amfani da fetur din in kona kaina ne.
A nan dai muka yi dariya, to dama ina sanye da wata rigar Fulani da take aljihu babba sai na sa fetur din a ciki. Haka na yi ta yawo da fetur din a cikin aljihuna har muka tafi kofar Maigishiri a Agadasawa muka zauna muna hira da wasu abokanmu, sai fetur din ya fashe a jikina.”

Mubaraka wanda dalibi ne dan aji biyar a Sakandiren Gwamnati ta Sabuwar kofa ya ce, “Dama da ashana a aljihuna sai abokin nawa ya ce in ba shi ita ya kunna min wuta. Ni kuma sai na jefa masa ina yi masa wasa, cewa ga ta ka kona ni tunda kai ba ka da hankali.
Shi kuma kamar wasa sai ya kyasta ashanar, nan da nan sai wuta ta kama a jikina. Na fada cikin kwatar unguwarmu kafin ta mutu jikina ya riga ya kone. Daga nan sai wasu ’yan unguwarmu da ke wurin suka riko ni suka kawo ni gida, yayata ta kai ni asibiti.”
Mubarak ya ce ya dauki abin a matsayin kaddara, kuma ya nemi hukuma da kada ta dauki wani hukunci a kan abokin nasa, ya yafe masa. “Shi ya sa lokacin da ’yan uwana suka nemi a kai rahoto ga ’yan sanda na ki amincewa. Na yafe masa, abin da nake fata shi ne Allah Ya ba ni lafiya,” inji shi.
Wani ganau wanda ya nemi a boye sunansa ya ce ba don tsautsayin yana kan Hassan ba, to da Mubarak ne zai kona kansa da kansa, “Tun farko lokacin da Mubarak ya taho da fetur ya furta cewa zai kone kansa cikin wasa. Hakan ya sa da Hassan ya ga fetur din ya zube masa a jiki ya dauki ashana yana yi masa wasa cewa zai kona Shi ,” inji ganau din.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here