sake haramta shigo da shinkafa
Nigeria
Rabo Haladu Daga Kaduna
Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya ta
sake haramta shiga da shinkifa ta
iyakokin da ba na ruwa ba.
A watan Oktoban bara ne dai hukumar ta ba da
damar shiga da shinkafar muddin za a biya
kudin fito kamar yadda ya dace.
Sai dai, a cewar hukumar, da farko kwalliya
tana biyan kudin sabulu amma daga watan
Janairun bana zuwa yanzu kudin shigar da ta
samu naira biliyan daya da miliyan dari shida
da tamanin bai kai abin da ya kamata a ce ta
samu ba, don haka take zargin ana fasa
kwaurin shinkafar.
Kakakin hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya
Wale Adeniyi ya shaidawa manema labarai ce wa a watan
Oktobar shekarar da ta gabata ne aka amince a
shigo da shinkafa ta iyakokin kasar, amma a
yanzu an soke wannan shawara.
Hakan na nufin an haramta shigo da ita ta
iyakokin kasa da kuma ta tashoshin jiragen
ruwa, an dauki matakin ne saboda an samu
rahoton an shigo da shinkafa ta tasahr jirgin
ruwa da ke Kwatano amma kuma ba a samu
kudaden shigar da su suka kai yawan abin da aka shigo da su ba.