Munga El-zakzaky Da Matarsa – Lauya Yusuf Ali

0
1629

IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna.

Labarai da dumi duminsu daga gidan gwamnati na Hassan USMAN Katsina Kawo Kaduna inda kwamitin binciken rikicin yan Shi\’a yake zama Lauyan wannan kwamiti Yusuf Ali, ya shaidawa kwamitin cewa a jiya Talata Jami\’an tsaron DSS dabke hedikwatar ta Abuja sun nuna masa jagoran harkar Shi\’a a Najeriya Sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky tare da matarsa Zinatu har ya yi magana da inda El-zakzaky ya shaida masa cewa shi bai san an kafa kwamiti ba.

Ya kuma shaida wa Lauya Yusuf Ali cewa yana son ya ga Lauyan Femi Falana.

A na nan a halin yanzu ana jin ta bakin Lauya don haka zamu kawo maku yadda lamarin ya kasance nan gaba kadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here