IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna
RUNDUNAR Sojan Najeriya sun bayar da sanarwar saka Ladan kudi Naira miliyan daya ga duk Wanda ya bayar da bayanin inda hafsan sojan da wasu suka sace a garin Kaduna yake.
Mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya shiyya ta daya mataimakin Daraktan yada labarai kanar Usman Abdul ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Rundunar sojan ta daya da ke garin Kaduna ta ce ga duk Wanda yake bukatar ya bayar da bayanin za\’a tabbatar da cewa ba a bayyana wa kowa ko shi wanene ba da ya bayar da bayanin.
In dai za\’a iya tunawa an sace hafsan sojan ne Kanar Isma\’ila Inusa, a ranar Asabar sun kuma tafi da shi wurin da ba a Sani ba.
Kuma bayanan da muka tattara daga wajen sojojin na shiyya ta daya sun ce babu wani bayani daga wadanda suka sace Hafsan na soja mai mukamin Kanar.
Shi dai Wanda aka sacen yana aiki ne da makarantar horar da sojoji da ke Jaji.
Rahotanni dai kamar yadda muka kawo maku a jiya na nuni da cewa an sace shi ne da misalin karfe 7:30 na yamma a kusa da mahadar matatar mai ta garin Kaduna inda ake kira Kamazo da ke Karamar hukumar Chukun.