Daga Usman Nasidi
HUKUMAR Tsaro ta Farin Kaya (Sibil Difens) a Jihar Nasarawa ta ce ta samu nasarar gabatar
da masu manyan laifuffuka 160 a gaban kotu inda aka yanke musu hukunci daga bara zuwa
watan Maris din bana.
Kwamandan Hukumar ta Jihar, Alhaji Bashir Lawal Kano ne ya bayyana haka a lokacin da
yake jawabi a wajen bikin kaddamar da sabon ofishin hukumar a yankin Nasarawa ta Kudu da aka gina a garin Keffi a karamar Hukumar Keffi da ke jihar.
Kwamandan ya ce hukumar ta cimma nasarar ne tare da hadin kan sauran jami’an tsaro, inda ya bukaci bangarorin jami’an tsaro a jihar su kara himma don kawo karshen ayyukan miyagun mutane.
Ya yaba wa hangen nesan Alhaji Usman Danladi Bagudu wanda ya gina ofishin, inda ya ce ba
ofishin kadai zai taimakawa ba, har da hukumar da yankin da jihar baki daya. Sai ya shawarci jami’an hukumar a yankin su yi amfani da sabon ofishin yadda ya kamata.
A jawabin Sanatan yankin, Sanata Abdullahi Adamu ya jinjina wa Alhaji Usman Danladi
Bagudu dangane da gudunmawar da ya bayar wajen tallafa wa harkokin tsaro a yankin inda ya yi kira da sauran masu hannu da shuni a yankin su yi koyi da halinsa.
A cewarsa Gwamnatin Tarayya ta himmatu sosai wajen kawo karshen rashin tsaro a kasa baki daya inda ya bukaci jami’an tsaro na farin kaya a yankin su yi amfani da ofishin yadda ya kamata.
Ya sanar da cewa zai ba da gudumawar Naira Miliyan daya da wasu kayayyakin gini don fadada ofishin.
Wakilin Sarkin Keffi, Alhaji Zakari Abubakar Kuyambanan Keffi da shgabannin kungiyoyi da na addini sun yi fatar alheri, inda suka yaba wa wanda ya gina ofishin kuma sun bukaci a yi
amfani da ofishin yadda ya kamata.