Rabo Haladu Daga Kaduna
SARKIN Kano Muhammadu Sanusi na II, ya shawarci \’yan kasuwa da su rinka kai
kudadensu ajiya bankuna maimakon barin su a shaguna, a wani mataki na rage
yawan asara a lokacin gobara.
Sarkin wanda ya katse ziyarar da yake yi a kasahen waje inda ya koma gida, ya yi kira ga
hukumomi a matakin jiha da gwamnatin tarayya da su tsananta bincike domin gano
musabbanin abinda ke janyo afkuwar gobara musamman a kasuwanni.
Rahotanni sun ce sama da shaguna 5,000 a gobara Kano kawai suka kone, inda kuma aka kiyasta cewa an rasa
dukiya ta biliyoyin Nairori.
A halin da ake ciki Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wani kwamiti domin bayar da shawara ta
gaggawa kan abin da ya kamata gwamnati ta yi wa \’yan kasuwar da bala\’in gobarar ya auka musu.