Rabo Haladu Daga Kaduna
RUNDUNAR \’yan sandan Najeriya, ta ce ta dukufa wajen magance matsalar tsaron da ake fama da ita a Jihar Kaduna, musamman sace-sacen jama\’a ana garkuwa da su don neman kudin fansa.
Tuni dai babban Sifeton \’yan sanda Solomon Arase ya umurci mataimakin shugaban \’yan sanda AIG na shiyya ta 7 AIG Ballah Nasarawa da ya koma Kaduna har sai al\’amurran tsaro sun inganta a jihar.
A \’yan kwanakin nan matsalar fashi da makami da kuma sace-sacen mutane ana garkuwa da su na ci gaba da ta\’azzara a jahar musamman a kananan hukumomin Jere da Kagarko da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja.
A kwanakin baya ne wasu al\’ummomin kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari a Jihar Kaduna suka koka da sabon salon fashi da makami da garkuwa da mutane da kashe-kashe
a yankunansu.
A cikin wata takarda da suka aike wa Gwamnan Jihar Kaduna, al\’ummomin sun bukaci gwamnati da ta kara kaimi don kawar da bata garin da suka addabi al\’umma.
Sai dai gwamnatin Jihar Kaduna ta ce tana sane da matsalar kuma ana daukar matakai na
hadin gwiwa tsakanin jami\’an tsaro don magance matsalar.