Daga Zubair Abdullahi Sada
GYARA fasalin wani abin da yake ya sami nakasu, ko yana neman lalacewa, ko ya gurbata ko abin da ya ki ci ya ki cinyewa, shi ake kira gyara al’amari. A hukumar Kwastan ta kasar Najeriya Kwamfuturola-Janar na Kwastan na kasa, Kanar Hameed Ali (mai ritaya), ya jaddada amanar yi wa hukumar ta kwastan gyaran fasali da gyaran fuska domin ta kasance tana kara bulbulo da kudaden shiga ga gwamnatin tarayya fiye da yadda ake samu a gwamnatocin baya.
Shugaban na kwastan ya yi wannan batu ne a Abuja a yayin da yake ganawar taro na farko da manyan jami’an kwastan bayan ya kama aiki. Ya bukaci jami’an da su yi aiki da shi domin su cimma nasarorin da ake neman su kawo don gaskata batun cewa, shugaba Muhammadu Buhari bai yi zaben tumun-dare ba da ya zabo shi.
Jami’in yada labarai (PRO) na hukumar ta kwastan ta kasa, Mista Wale Adeniyi ne ya sanar wa manema labarai haka cikin wata takarda da ya aike masu a rubuce.
Shugaban na kwastan ya ce, shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da ya nada shi bisa wannan mukami a ranar 27 ga watan Agustar 2005, sai da ya umurce shi da abubuwa uku ya ce,’’ ka tafi hukumar kwastan, ka gyara kwastan, ka yi wa kwastan gyaran fuska, ka bido tare da karin kudaden shiga ga kwastan, zas sauki. Ba na ganin cewa, hakan bai yiwuwa, ba na tsammanin cewa, al’amarin yana da wahalar aiwatarwa. Ya yi maganarsa kai tsaye, kuma ina ganin tare da yin imani cewa, wannan shi ne abin da ya sanya dukanku kuke a nan domin ku aiwatar da su’’. Yake gaya wa manyan jami’an kwastan na kasa.
Daga nan sai Kanar Hameed Ali ritaya, ya nemi goyon bayan dukan manyan jami’an da biyayyarsu a gare shi kan su hada hannu da shi domin bin aniyarsa ga hukumar kwastan ta Najeriya don fitar da hukumar ga kunya ta zama ma’aikata mai nagartar aiki.
Tun farko a jawabinsa, mataimakin kwanfuturola-janar na hukumar da yake aikin shugaban idan babu shugaba, Mista John Atte a yayin da yake mika kundin aikin hukumar kwastan ga sabon shugaban, sai da ya fadi tarihin hukumar ta kwastan a takaice, kuma ya bai wa sabon shugaban kwastan Hameed Ali tabbacin zai ga biyayyar manyan jami’an kwastan da yaransu, wato kananan ma’aikata wajen ganin an sami kawar da yin simogal da samar da karin kudaden shiga da makamantan wadannan ayyukan nasu, domin ci gaban Najeriya baki ]aya.
Idan ba a manta ba dai an haifi Kanar Hameed Ali ne a garin Dass da ke karamar hukumar Dass da ke Jihar Bauci a ranar 15 g watan Janairun 1955. Ya yi makarantar NDA da ke garin Kaduna a shekarun 1974 zuwa 1977, ya kuma tafi jami’ar Jihar Houston da ke Huntsville Texas a kasar Amurka a shekarar 1980 zuwa 1984, yana da digirinsa na daya da na biyu a fannin ‘Ilimin Laifuffuka’’, kuma yana da Satifiket na Ilimi na NDACE.
Ayyukan da ya gabatar na soja kuwa sun hada da Kantoman Mulkin Soja na Jihar Kaduna a shekarar 1996 zuwa 1998 da tirenin na Kanar TRADOC da ke Minna a 1998. A can baya kafin wadannan mukamai, Hameed Ali ya rike shugaban ofisoshin soji II a hedikwatar sojoji a 1981 zuwa 1982 da irin wannan mukamin na II a rundunar sojojin ta I da ke Kaduna a shekarar 1992 da kuma kwamanda na hukumar bincike ta musamman da ke Apapa a garin Ikko a shekarar 1994 zuwa 1996.