JABIRU A HASSAN, Daga kano.
Kungiyar tabbatar da shugaban ci nagari watau \’ Good Leadership Initiative\’ ta yi kira ga shugabannin kasashen nahiyar Afirka da su daina yin amfani da karfin ikon da suke dashi wajen dawwama akan mulki, domin kaucewa jefa nahiyar cikin rikici kamar yadda ake gani a wasu kasashen nahiyar.
Shugaban kungiyar Alhaji Ahmad Buhari Baba shine ya sanar da haka a karshen wani taro da kungiyar tayi mai taken \’ Neman dawwama a kan mulki\’ wanda aka gudanar a kano, inda yace neman dawwama kan mulki abune mai hadari ga tsarin mulki a wannan zamani, sannan idan ba\’a sami sa\’a ba sai a jefa kasa cikin wani hali na fitina.
Bugu da kari, shuagab kungiyar ya roki shugabannin kasashen nahiyar Afirka dasu rika neman mulki bisa la\’akari da bukatun al\’umominsu maimakon nuna karfin mulki domin neman dawwama a mulki, inda kuma daga karshe yayi fatan cewa shugabannin kasashen nahiyar Afirka zasu hada hannu wajen tabbatar da dawwamammen zaman lafiya a nahiyar, tareda jaddada cewa kungiyar zata