Imrana Abdullahi Daga Kaduna Nijeriya
SHUGABAN kungiyar yan kasuwar Abubakar Gumi da ke Kaduna Alhaji Adamu Ibrahim Mai Shinkafa, ya bayyana batun cewa wai dan kasuwa Dangote bai karawa kayansa kudi ba da cewa yaudara ce kawai.
Adamu Ibrahim Mai Shinkafa, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani shirin tattaunawa a kan harkokin kasuwanci a gidan Talbijin na DITV da ke a garin Kaduna.
Mai Shinkafa, ya ce indai babu yaudara ya dace shi Dangote ya fito ya tara manema labarai ya fayyace wa duniya cewa bai karawa kayansa kudi ba.
\”Saboda ni a matsayina na shugaban yan kasuwa wasu daga cikin yan kasuwar da suka kasance Diloli ne da suke sayen kayan Dangote sun gaya mini cewa sun samu kari, wasu ma sun gaya mini cewa sun biya kudin kaya ga kamfanin Dangote tun kafin a samu kari amma da suka je dauka sai aka ce ba za su dauki kayan ba sai sun yi karin kudi kamar yadda farashin yake a lokacin da suka zo daukar kayan, to ina batun bai yi wa kayansa kari ba\”.
A game batun cinkoson kasuwar Abubakar Gumi na rashin wuraren yin fakin don sauke kayan da yan kasuwa suke kawowa ya bayyana lamarin da cewa laifin gwamnati ne domin tun farko an gina kasuwar ne amma ba hanyar shiga da mota domin sauke kaya.
Kai ko da wurin fakin mashin din hawa wahala yake don haka ya dace gwamnati ta gyara lmaarin saboda a wasu wuraren sai mutum daya ya gina kasuwarsa amma ya yi wurin fakin, amma kuma gwamnati ta kasa.
Ya kara da cewa ya dace duk masu son sanin ko Dangote ya yi wa kayansa kari ko a\’a to yaje ya tambayi Dilolinsa domin sanin yawan karin da aka yi wa kayan kamfaninsa.
Ya kuma yi kira ga daukacin yan kasuwa da su ci gaba da yi wa gwamnan Jihar Kaduna Addu\’ar Allah ya bashi ikon ba yan kasuwa kudin bashin da ya ce zai ba yan kasuwar Jahar Kaduna domin ciyar da Jihar gaba.
A game da batun Gobara kuwa Mai Shinkafa ya bayyana lamarin da cewa mafi akasarin Gobarar laifin lamfanin samar da wutar lantarki ne a mafi yawan lokuta don haka hukumar ta kara daukar matakan kiyaye wa domin jin dadin jama\’a baki daya.