YAN SANDA SUN KAMA DILLALIYAR JARIRAI

0
1460

DAGA USMAN NASIDI 

Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta samu nasarar kama wata mata mai suna Talatu Dauda mai kimanin shekara 37 a duniya wanda ta fito daga Jihar Filato bisa zarginta da sace wani yaro dan shekara daya da wata biyar wanda ta sayar da shi a kan Naira dubu 200.


Ana zargin Talatu da sayar da yaron ga wata
mace mai suna Ann-Okechuku mai kimanin
shekara 50 a wadda take zaune a Jihar Enugu da
ke kudancin Najeriya, wadda ita ma ta sayar da
yaron ga wata mata mai suna Hannah Ashaku
mai kimanin shekara 41 ’yar asalin Jihar Benuwai.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi DSP
Haruna Muhammed ne ya bayyana haka a wata
sanarwa da ya raba ga manema labarai a Bauchi.

Ya ce dukkan wadanda ake zargin suna hannun
rundunarsu ta Jihar Bauchi kuma suna ci gaba
da ba da bayanai, da zarar an kammala bincike
za a gufanar da su a gaban kotu.


Da take zantawa da wakilinmu, mahaifiyar yaron Ramatu Musa ta ce tana zaune a cikin gida sai Talatu Dauda ta zo ta dauki Muhammadu Najasi ta gudu da shi, inda ta sayar da shi a kan Naira dubu 200 ga wata mata a Kudu.


Ta ce “Muhammadu ya shafe sama da kwana 20
a hannun wadda ta sace shi da wadda ta saye
shi. Kuma lokacin da abin ya faru ni da mahaifinsa mun kai rahoto ga ’yan sanda a
Bauchi daga bisani sai muka samu labarin cewa
an sayar da yaron, amma an kama Talatu Dauda
tana hannu, mun tafi da ’yan sanda daga nan
Bauchi zuwa garin Enugu kuma an samu nasarar
kama Talatu tare da mata biyu, wannan shi ne
abin da zan fada a takaice.”


Ta ce sun dauki tsawon lokaci suna neman
Talatu Dauda kafin su samu labarin cewa ta jima
tana safarar jarirai daga Bauchi zuwa kudancin
kasar nan.


“Wannan abin da ya faru ya zamo min darasi, kuma daga yanzu babu wanda zan sake
amincewa da ita in ba ta dana ta rike.


Lokacin da aka gudu da Muhammadu Najasi akwai mutane da dama da suka yi ta yada jita-jitar cewa wai na sayar da dana ne, kafin Allah Ya
bayyana gaskiyar abin da ya faru.

 


Ina godiya ga Allah, sannan ina mika godiya ga Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi da sauran al’umma da suka taimaka mana da addu’o’i har Allah Ya tona asirin Talatu da wadanda ta sayar musu da shi,” inji ta. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here