JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
KUNGIYAR tabbatar da shugabanci nagari wato \’ Good Leadership Initiative\’ ta yi kira ga shugabannin kasashen Nahiyar Afirka da su daina yin amfani da karfin ikon da suke da shi wajen dawwama a kan mulki, domin kauce wa jefa Nahiyar cikin rikici kamar yadda ake gani a wasu kasashen Nahiyar.
Shugaban kungiyar Alhaji Ahmad Buhari Baba shi ne ya sanar da haka a karshen wani taro da kungiyar ta yi mai taken \’ Neman dawwama a kan mulki\’ wanda aka gudanar a Kano, inda ya ce neman dawwama kan mulki abu ne mai hadari ga tsarin mulki a wannan zamani, sannan idan ba a sami sa a ba sai a jefa kasa cikin wani hali na fitina.
Bugu da kari, shugaban kungiyar ya roki shugabannin kasashen Nahiyar Afirka da su rika neman mulki bisa la\’akari da bukatun al\’umominsu maimakon nuna karfin mulki domin neman dawwama a mulki, inda kuma daga karshe ya yi fatan cewa shugabannin kasashen Nahiyar Afirka za su hada hannu wajen tabbatar da dawwamammen zaman lafiya a Nahiyar.