Kungiyoyin Ayyukan Gayya Za Su Taimaka Wa Gwamnatin Jihar Kano

0
1148

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

SHUGABAN kwamitin koli na kungiyoyin ayyukan gayya na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Garba Aminu Kofar Na\’isa ya ce kungiyoyin ayyukan taimakon kai da kai za su taimaka wa gwamnatin Jihar Kano wajen tsaftace muhalli da yashe magudanun ruwa ganin yadda damina take kara matsowa.

Ya yi wannan bayani ne a ganawarsu ga wakilinmu, inda ya sanar da cewa kungiyoyin aikin gayya suna taka muhimmiyar rawa wajen tsaftace muhalli da share magudanun ruwa da kuma gyaran makabartu da sauran muhimman ayyuka na bunkasa rayuwar al\’umma kuma bisa sa kai.

Sannan ya tabbatar da cewa gwamnatin Jihar Kano tana kokari kwarai wajen ganin ana tsaftace muhalli wanda hakan ce ta sanya aka ware kowace Asabar ta kowane karshen wata a matsayin ranar tsaftar muhalli, wanda kuma a cewar sa hakan ya taimaka sosai wajen tsaftace binin Kano da kuma yankunan karkara kamar yadda ake bukata.

Alhaji Ibrahim Garba ya yi amfani da wannan dama inda ya yi albishir ga kungiyoyin ayyukan gayya da ke fadin Jihar ta Kano cewa gwamnatin jihar na tare da su dari bisa dari kan wannan al\’amari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here