JABIRU A HASSAN,Daga Kano.
WANI matashin dan siyasa Alhaji Garba Baban Larai ya yi yi kira ga al\’ummar Nijeriya da su kara nuna juriya da hakuri bisa halin da kasa take ciki kafin al\’amura su daidaita nan gaba kadan.
Ya yi wannan kiran ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai, inda ya kara da cewa idan aka kara hakuri, dukkan al\’amura za su zamo tarihi musamman idan aka yi la\’akari da matakan da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake dauka na kawo sauyi a kasar nan.
Sannan ya nunar da cewa Nijeriya ta sami kanta cikin wani mawuyacin hali sakamakon mulki na son zuciya da aka dade ana yi mata, wanda a cewarsa, dole ne sai an yi hakuri kafin a cimma gyara kamar yadda kowa yake tsammani.
Alhaji Baban Larai ya sanar da cewa kada \’yan Nijeriya su dauka cewa za a iya gyara dukkanin barnar da aka yi cikin lokaci kankane, wajibi ne a bi a hankali kafin a daidaita komai musamman ganin cewa Nijeriya kasa ce babba kuma mai yawan al\’umma a kowane bangare, inda daga karshe ya yi fatan cewa za a kara bai wa gwamnatin tarayya goyon baya.