JABIRU A HASSAN,Daga Kano.
SHUGABAN rukunin gonaki na \’Musani Farms\’ da ke Kano Alhaji Musa Sani ya shawarci gwamnatin tarayya da na jihohi da su samar da kayan aikin gona ga manoman kasar nan ta yadda za su bunkasa noman su don wadata kasa da abinci.
Alhaji Musa Sani ya yi wannan tsokaci ne a tattaunawarsu da wakilinmu dangane da shirin bunkasa noma na gwamnatin tarayya, inda ya sanar da cewa samar da kayan aikin gona da wuri zai taimaka sosai wajen yin aiki da wuri ta yadda za a sami damina mai albarka.
Ya ce ana samar da kayan aikin gona kamar takin zamani da irurrukan shukawa da kuma magungunan feshi a kurarren lokaci wanda a wasu lokutan ma sai damina ta yi zurfi ake raba taki kuma hakan na jawo faduwa walau a damina ko rani ga manoma tare da fatar cewa za a gyara wannan matsala.
Daga nan sai ya tabbatar da cewa idan aka bai wa manoman kasar nan goyon baya da taimako za su iya samar da wadataccen abinci a kasa har ma a rika fitar da shi zuwa kasashen waje kamar yadda muke gani a wasu kasashen.