A Kano An Gano Ma\’aikatan Bogi Dubu Bakwai

0
1590

Jabiru A Hassan,  Daga kano.

Gwamnatin jihar kano ta gano ma\’aikatan bogi  sama  da dubu bakwai a  ma\’aikatu daban-daban na jihar.

kamar yadda shugaban ma\’aikatan jihar, Alhaji Muhammadu Na\’iya  a wata ganawa da ya yi da manema labarai.

Ya ce  an gano ma\’aikatan ne sakamakon aikin tantancewar da aka yi,  kuma za\’a  tabbatar da cewa an yi hukumci dai dai gwargwadon laifukan wadanda suke da hannu cikin wannan lamari  domin ganin an tsaftace harkokin ma\’aikata a jihar.

Haka kuma ya bayyana cewa gwamnati ta sami rarar kudade masu yawa sanadiyyar wannan tantancewa da akayi, tare da jaddada cewa da yardar  Allah za\’a ci gaba da tantance ma\’aikatan jihar ta yadda za\’a kammala  tattara sahihan alkaluma a  kan ma\’aikatau gwamnati a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here