An yi jana\’izar mutane 44 a Taraba

0
1247

Rabo Haladu Daga Kaduna

AN yi jana\’izar  mutane kimanin arba\’in da hudu  a jihar Taraba  wadanda wasu \’yan bindiga suka kashe
a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Gashaka.
A ranar Lahadi da dare ne dai zuwa wayewar garin Litinin, maharan suka far wa kauyukan da bindigogi da kuma adduna, inda suka yi kashe-kashe da kone-kone sannan suka sulale.
Hukumomi dai na cewa sun dukufa domin bincike da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu a aika-aikar.
Jihar ta Taraba dai ta sha fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini musamman a kananan hukumomin Wukari da Ibi, amma ba kasafai ake samun tarzoma a yankin na Gashaka ba, inmda aka yi kashe-kashen na
baya-bayan nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here