An Sami Faifan Bidiyon \’Yan Matan Chibok

0
1259

Rabo Haladu Daga Kaduna

GIDAN talabijin na CNN ya samu wani faifan bidiyo mai dauke da hotunan \’yan mata
guda 15 da ake kyautata zaton wasu ne daga cikin \’yan mata fiye da 200 da aka
sace a garin Chibok na Jihar Borno.
A ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne dai wasu wadanda ake kyautata zaton \’yan Boko Haram
ne suka sace \’yan matan daga makarantar sakandare ta garin na Chibok.
Kafar yada labaran ta ce ta a watan Disamba ne ta samu faifan bidiyon daga hannun wani
wanda yake kokarin ganin an sasanta tsakanin \’yan kungiyar Boko Haram da
gwamnatin tarayya wajen sakin \’yan matan.
A cikin faifan bidiyon dai, ana iya ganin \’yan mata guda 15 sanye da bakaken hijabi, kuma
suna jingine da wani gini mai launin ruwan dorawa.
An jiyo kuma wata muryar namiji yana tambayar sunayensu ɗaya bayan ɗaya da kuma
wurin da aka sace su.
Kafar yada labaran ta CNN ta ruwaito cewa faifan bidiyon ya kare ne da ɗaya daga cikin
\’yan matan, a inda take sanar da gwamnati cewa suna nan lafiya tare da mika wasu bukatu
da suke bukatar gwamnati ta biya wa \’yan kungiyar ta Boko Haram.
Ministan yada labarai  Lai Mohamed ya shaida wa CNN cewa sun samu
bidiyon kuma suna nazari a kansa.
Rahotan na CNN ya nuna cewa har zuwa watan Disambar shekarar da ta gabata, wasu daga
cikin \’yan matan na Chibok suna raye.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here