Jabiru A Hassan, Daga Kano.
YARA hudu sun mutu a cikin wata mota wadda aka ajjiye cikin wani kango a unguwar sharada cikin birnin kano, inda kuma an kyautata zaton cewa zafi ne ya yi sanadiyyar mutuwar yaran.
Wakilin mu ya ruwaito cewa yaran masu kimanin shekaru uku zuwa biyar sun shiga motar ne tun da safiya amma suka kasa fitowa har wajen karfe biyar na yammaci lamarin da ya sanya zafi yayi sanadiyyar mutuwar su su duka hudun.
Kakakin rundunar \’yan sandan jihar ta kano, Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya bukaci al\’uma da su kara lura da yanayin zirga-zirgar \’ya\’yan su tare da tabbatar da cewa ana kiyaye ajjiye ababen hawa ta yadda ba zasu zamo barazana ga rayuwar yara ba.