Rabo Haladu Daga Kaduna
Shekaru uku bayan rufe hanyar damaturu zuwa biu da sojojin sukai an buɗe ta batare da bata lokaciba.
Itadai wannan babar hanya itace ta hada manyan jihohin Yobe da Borno.
An rufe hanyar saboda rikicin Boko Haram da
ya tilastawa mazauna garuruwa da dama dake
kan hanyar yin gudun hijira.
Buɗe hanyar ya bada dama ga mutane suka
koma gidajensu a garin Buni Yadi, wanda \’yan
Boko Haram suka taɓa kwacewa.
Babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar
Tukur Buratai ya ce, an bude hanyar ce saboda
ingantar sha\’anin tsaro.
Hanyar dai ta na da muhimmanci ga tattalin
arzikin yankin da ya haɗa jihohin Yobe da
Borno, da kuma Adamawa