NLC Na Shirin Yin Fito-Na-Fito Da Sanatoci Kan Sayen Motoci 108

0
1135

Rabo Haladu Daga Kaduna

KUNGIYAR kwadago ta Najeriya NLC, ta ce za ta yi fito-na-fito da mambobin majalisar dattawa idan har ba su mayar da
motocin kawar da aka saya musu ba.
Kungiyar dai ta yi watsi da matakin da sanatocin suka dauka na karbar motocin kirar Toyota Land Cruiser guda 108 wadanda za a bai
wa kowanne Sanata daya, bayan kuma sun karbi bashin motoci a watan Augustan bara inji kungiyar.
NLC ta ci gaba da cewa wannan abin kunya ne,saboda kwamitocin majalisar da aka nada sun ce ba za su iya wasu ayyuka ba saboda
babu kudi, amma kuma yanzu an ba su motoci sun karba.
Kungiyar ta ce su a matsayinsu na \’yan kasa suna ganin wannan abu sam bai dace ba, saboda an kara wa motocin kudi, inda a da aka
ce kowacce mota za a siyo ta a kan kudi Naira Miliyan 17, amma kuma sai ga shi yanzu an kara zuwa Naira Miliyan 35.
Abin tambayar da \’yan Najeriya za su yi shi ne a ina aka samo wadannan makudan kudade bayan ba a amince da kasafin kudi ba? inji
NLC.
Kungiyar ta ce abin da Kakakin majalisar dattawan Aliyu Sabi Abdullahi ya fake da shi ne, na cewa, wai masu bai wa shugaban kasa
shawara na amfani da motoci kirar Jeep, to me ya sa sanatoci ba za su yi ba, shin ana so ne su  tafi a kafa? Wannan magana kungiyar ta ce
abin dariya ne kuma wasan yara ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here