Jabiru A Hassan, Daga Kano.
AN bayyana cewa siyasar da ake yi a halin yanzu ba ta akidar ci gaban kasa ba ce ana yi ne a matsayin wata hanya ta azurta kai da tara abin duniya.
Wannan tsokaci ya fito ne daga manyan baki da suka halarci taron tunawa da Marigayi Malam Aminu Kano wanda aka saba yi duk shekara a cibiyar nazarin dimokuradiyya da ke Kano.
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari wanda ya yi dogon jawabi a wajen taron, ya ce Malam Aminu Kano ya yi zamanin sa ne bisa akidar taimaka wa al\’umma don haka ne za a ci gaba da tunawa da shi har abada saboda rayuwarsa ta amfani al\’umma kamar yadda ake gani a yau.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje, wanda mataimakinsa Farfesa Hafizu Abubakar ya wakilta, ya bayyana Marigayi Malam Aminu Kano a matsayin jagoran talakawa wanda ba ya tunanin abin duniya, inda ya kara da cewa wajibi ne shugabannin yanzu su yi koyi da marigayin.
Ita ma \’yar ta Malam Aminu kano, Hajiya Maryan Aminu Kano ta nunar da cewa \’yan siyasar wannan zamani ba sa yin koyi da mutane irin su Malam Aminu Kano.