Fetur Yana Samuwa A Jihar Kano

0
1121

 

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

AN fara samun saukin matsalar man fetur a Jihar Kano saboda yadda mafiya yawan gidajen mai da ke jihar suna sayar da shi a farashin da ba na gwamnati ba ganin cewa mai tsada suke sayowa su sayar don kada harkar sufuri ta durkushe baki daya.

Wakilinmu wanda ya duba yadda gidajen mai suke sayar da mai, ya ruwaito cewa  ana samun dillalai masu kokari suna samar da mai a manyan hanyoyi kamar hanyar Kano zuwa Katsina  da Kano zuwa Daura da hanyar Kano zuwa Abuja da hanyar Kano zuwa Maiduguri da kuma sauran hanyoyi da ake bi zuwa sauran sassa na kasar nan.

A hanyar Kano zuwa Katsina wakilinmu ya zanta da manajan gidan mai na Challawa Oil And Gas Alhaji Mahi Haruna, wanda ya bayyana cewa suna kokarin samar da mai ne ganin cewa wannan hanya babbar hanya ce wadda kuma ta hada kasar nan da wasu kasashe na Afirka.

Bisa ga dukkanin alamu dai ana samun saukin karancin man fetur musamman ganin cewa gidajen mai da suka dade ba su sayar da mai ba yanzu suna sayarwa, sannan ana samun saukin  yin tafiye-tafiye da sauran zirga-zirgar yau da kullum.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here