Jabiru A Hassan, Daga kano.
Sakamakon Iftila\’in gobarar da ta faru a kasuwar sabon Garin Kano kwanakin baya, yanzu haka dai \’yan kasuwar sun cimma kashi 70 daga cikin dari na aikin sake ginin rumfunan su da suka kone.
Wakilin mu wanda ya ziyarci kasuwar, ya ruwaito cewa \’yan kasuwar suna kokari matuka wajen gyaran rumfunan su , sannan wasu ma har sun kammala aikin gyaran rumfunan nasu harma sun fara sanya kaya domin ci gaba da kasuwancin su kamar yadda aka saba.
Tuni dai kungiyar \’yan kasuwar ta Sabon Garin Kano ta bayyana godiyar ta ga gwamnatin jihar kano saboda baiwa \’yan kasuwar dama da tayi na su sake ginin rumfunan su da kansu kamar yadda suka nema tun da farko.