An Sace Matan Dan Majalisar Dokokin Jihar Kano

0
1193

Jabiru A hassan, Daga Kano.

A daren Litinin din data gabata ne, wasu \’yan bindiga dadi wadanda ake zaton cewa masu  garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da matan dan majalisar dokoki ta Jihar Kano mai wakiltar  karamar hukumar Kibiya Alhaji Garba Shehu Fammar su biyu.

Shaidun gani da ido sun  bayyana cewa \’yan bindigar wadanda yawansu yakai 40, sun dira a garin na kibiya ne da misalin karfe 2 na dare inda suka yi ta harbi a sama kafin su kutsa kai cikin gidan su debo matan guda biyu.

Wani wanda ya hangi lokacin da \’yan bindigar suke yin harbe-harbe, ya ce  maharan sun yi wa gidan dan majalisar kawanya tare da bude wuta a sama domin tsoratar da mutane masu zuwa ceto, inda sanadiyyar hakan aka harbi wasu \’yan Banga guda biyu kuma suka mutu sanadiyyar harbin da aka yi masu.

Kakakin rundunar \’yan sanda ta Jihar Kano Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa tuni rundunar ta fara gudanar da bincike domin gano \’yan bindigar, sannan shi kansa kwamishinan \’yan sandan jihar Alhaji Maigari Dikko ya ziyarci garin na Kibiya inda ya duba yadda harin ya gudana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here