Daga Usman Nasidi
KIMANIN mutane guda takwas sun rasu inda mutane guda 12 sun raunata dalilin harin kunar bakin wake wanda ta auku a sansanin \’yan gudun hijira a garin Banki na Jihar Borno.
An bayyana wannan matan kunar bakin wake guda biyu sun kashe mutane takwas inda masu yawancin kwana a cikin sansanin \’yan gudun hijira sun sami raunuka daban-daban.
Wadannan \’yan gudun hijira suna zaune ne cikin sansanin saboda ta’addancin kungiyar yan Boko Haram.
A hira da wakilinmu yayi da wani mutum mai suna Khalid Aji da kuma dan kungiyar Grassroots Community Security Group, wanda dake a garin Konduga ya ce: “Matan kunar bakin wake guda biyu, wadanda, muke tunanin wadanda suka fake ne a cikin yan gudun hijira, sun kashe kansu, inda suka tashi bama-bamai a cikin sansanin \’yan gudun hijira.
“Harin kunar bakin wake na farkon ya auku a daidai karfe 8 da safe, inda na biyu ya auku bayan mintuna kadan. Mutane guda takwas sun mutu, inda mutane guda 12 sun raunata.”
Mista Aji ya bayyana cewa \’yan kungiyarshi, sun taimaki masu rauni. Kuma, wani babban ma’aikacin hukumar Kwastam ya tabbarta da hakan, inda yake cewa mutane guda 15 ne sun raunata.
Wannan garin Banki, yana da nisa daga Maiduguri da ya kai kimanin kilomita 120 ne daga babban birnin jihar.