Ya Bai Wa Ministan Wasanni Da Gwamnatin Tarayya Shawara

    0
    1089

    Jabiru A Hassan, Daga Kano.

    WANI kwararre kan harkar kwallon kafa kuma wanda ya yi fice kan aikin horar da \’yan wasan kwallon kafa Malam  Mustapha Umar  Tallo  Gwarzo  ya ce  lokaci ya yi da za a sasanta rikicin da ya dabaibaye hukumar kula da wasan kwallon kafa  ta kasa ta yadda Nijeriya za ta cimma nasarori  ta fuskar kwallon kafa.

    Malam  mustapha Tallo ya yi wannan bayani ne a ganawarsu da wakilinmu, inda ya sanar da cewa yana da kyau a sasanta dukkan bangarorin da suke rikici da juna kan jagorancin hukumar  kula da kwallon kafa ta kasa domin a hada hannu wajen tunkarar kowane irin kalubale da ka iya  jawo koma baya a fannin wasan kwallon kafa a kasar nan.

    Sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bai wa masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa damar tsara yadda za a tafiyar da hukumar kwallon kafa ta kasa  da kuma  yadda gwamnati za ta rika kula da sha\’anin wasan kwallo ba tare da  an sami matsala ba, wanda hakan shi ne kadai zai sanya kwalliya ta biya kudin sabulu.

    Malam Mustapha Umar Tallo ya kuma shawarci hukumar kula da kwallon kafa ta kasa da ta sake bai wa Steven Keshi damar jagorantar kungiyar kwallon kafa ta kasa  maimakon dauko mai horaswa daga waje  musamman ganin cewa Steven Keshi  yana da cikakkiyar kwarewa a fannin horar da \’yan wasa idan aka dubi tarihinsa, inda daga karshe ya yaba wa shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Alhaji  Kabiru Baita da mai horar da \’yan wasan Muhammadu Baba Ganaru da kuma ita kanta gwamnatin Jihar Kano bisa yadda aka hada hannu ana tafiyar da kungiyar cikin nasara.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here