\’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Matan Dan Majalisa

    0
    1279

    Jabiru A hassan, Daga Kano.

    A daren litinin din da ta gabata ne, wasu \’yan bindiga dadi wadanda ake zaton cewa masu  garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da matan dan majalisar dokokin  jihar kano mai wakiltar  karamar hukumar Kibiya Alhaji Garba Shehu Fammar su biyu.

    Shaidun gani da ido sun  bayyana cewa \’yan bindigar wadanda yawansu yakai 40, sun dira a garin na kibiya ne da misalin karfe 2 na dare inda suka yi ta harbi a sama kafin su kutsa kai cikin gidan su debo matan guda biyu.

    Wani wanda ya hangi lokacin da \’yan bindigar suke yin harbe-harbe, yace  maharan sun yiwa gidan dan majalisar kawanya tareda bude wuta a sama domin tsoratar da mutane masu zuwa ceto, inda sanadiyyar hakan aka harbi wasu \’yan Banga guda biyu su kuma  mutu sanadiyyar harbin da aka yi masu.

    Kakakin rundunar \’yan sanda ta Jihar Kano Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa tuni rundunar ta fara gudanar da bincike domin gano \’yan bindigar, sannan shi kansa kwamishinan \’yan sandan jihar Alhaji Maigari Dikko ya ziyarci garin na kibiya inda ya duba yadda harin ya gudana.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here