YAN SANDA SUN KAMA BARAYIN SHANU 23 A FILATO

0
1189

Daga Usman Nasidi 

Yan sandan Najeriya sun kama barayin Shanu guda 23 a jiya 20 ga watan Afrillu na 2016, Yan sandan Jihar Filato sun nuna barayin Shanu guda 23 wadanda suka kama inda suka gurfanar dasu a gaban kotu akan laifukan satar Shanu da kuma rike makamai.
A inda ake nuna wadanda ake zargin a Hedikwatar Yan sanda ta jihar, Kwamishinan yan sanda Adekunle Oladunjoye ya bayana cewa ” A ranar 3 ga watan Afrillu na 2016, kimanin karfe 1 na dare, rundunar yan sanda ta musamman ta kama wadansu mutane guda 5 wadanda ake zargin cewa Barayin shanu a karamar hukumar Wase dake Jihar Filato.
Ya bayyana cewa ana gurfanar da Alhaji Lawal Idris ( Goma), Mohammadu Yusuf, Musa Abubakar, Buba Ishaku da Idris Yusuf.

Kwamishinan ya bayyana cewa an kama harsashi mai yawa a hannun wadanda ake zargin, sannan kuma an kama su da mashina wadanda ake zargin sataowa sukayi.  An kuma kama su da wayar salula guda 9 Wadanda ake zargin daman ana neman su akan zargin aikata laifuka daban-daban.

Rundunar yan sanda ta sha alwashin tabbatar da cewa anyi adalci kamar yadda aka alkawurranta.

Kwamishina yan sanda na jihar ya shawarci al’umma dasu kasance masu bin doka da Oda, domin yan sandan jihar shirye suke da su hukunta dukkanin masu neman tada zaune tsaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here