Rabo Haladu Daga Kaduna
SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a fitar da abinci tan 10,000 daga rumbun ajiyar abinci na kasa
domin raba talakawa a yunkurinsa na saukaka wa jama\’a tsadar kayan abinci da ake fuskanta.
Shugaba Buhari ya kuma bayar da umarni ga ma\’aikatar aikin gona ta tallafa wa masu jini a jika; maza da mata da ke zaune a sansanonin
\’yan gudun hijira su koma gona domin a haɓaka samar da abinci.
Wata sanarwa da ke dauke da sa hannun kakakin shugaban kasa Malam Garba Shehu ta kuma ce, shugaban yana
ɗaukar matakai na ganin cewa jama\’a sun samu saukin rayuwa.
Gwamnatin kuma ta ce halin da jama\’a suke ciki yanzu sakamako ne na rashin shiri domin gobe, cin hanci da rashawa, da
kuma rikicin Boko Haram.
Shugaba Buhari ya kara da cewa gwamnati tana daukar matakai na saukakawa jama\’a kuncin rayuwa, wadanda suka hada da samar
da tallafin N5000 ga mutanen da ba su da galihu.
Gwamnatin ta ce akwai wani shiri na daukar matasa masu shaidar karatun digiri 500,000 aikin koyarwa na sa-kai, inda
gwamnatin tarayya za ta rika biyansu yayin da suke ci gaba da neman aiki.
Akwai kuma wani shiri na koyar da sana\’a ga matasa 370,000, kuma za a rika biyansu yayin da suke koyon sanao\’i.