Ya Yaba Da Kokarin \’Yan Banga

0
1187

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

WANI jigo a kungiyar Banga ta kasa watau  VGN , Malam Muktar Dahiru S. Doka ya  jijnjina wa  \’ya\’yan kungiyar saboda sadaukar da kai da suke yi wajen taimaka wa jami\’an tsaro domin tabbatar da dorewar zaman lafiya a kasar nan.

Ya yi wannan godiya ne a ganawar sa da wakilinmu yayin da yake duba yadda \’yan kungiyar ta VGN suke gudanar da ayyukan su na kare lafiya da dukiyoyin jama\’a  a daya daga cikin manyan kasuwannin Jihar Kano.

Malam Muktar S. Doka ya sanar da cewa kungiyar VGN tana kokari kwarai da gaske wajen taimaka wa hukumomin tsaro a kowane lungu da sako na wannan kasa tamu, don haka yana da kyau al\’ummar Nijeriya  su fahinci cewa \’yan Banga suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro da bunkasa zaman lafiya a kasar nan  kuma bisa sa kai.

Ya yi amfani da wannan damar inda ya yaba wa babban kwamandan kungiyar ta VGN na kasa wato Alhaji Ali Sokoto  da mataimakansa saboda yadda yake jagorantar kungiyar bisa sanin ya kamata, tare da yin kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here