Jabiru A Hassan, Daga Kano.
GWAMNAN Jihar Kano Dokta. Abdullahi Umar Ganduje ya gode wa al\’ummar jihar saboda goyon bayan da suke ba shi wanda hakan ya tainaka wajen samun nasarori a gwamnatinsa.
Ya yi wannan tsokaci ne a daren Lahadin da ta gabata bayan dawowarsa daga kasa mai tsarki inda ya duba yanayin masaukan alhazan da aka samar ga maniyyatan jihar, inda ya nunar da cewa tsakanin sa da al\’ummar Jihar Kano sai godiya da girmamawa.
Dokta Ganduje wanda ya sami tarba daga mataimakinsa Farfesa Hafizu Abubakar da kwamishinoni da sauran manyan kusoshin gwamnatin jihar, ya danganta nasarorin da gwamnatinsa ke samu da goyon bayan da yake samu daga abokan aiki da kuma daukacin al\’ummar jihar.
Daga nan sai ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aikace-aikace na ci gaban Jihar Kano kuma bisa yin la\’akari da bukatun al\’umma a kowane fanni na zamantakewar jama\’a.