Gobara Ta Lashe Shaguna 30 A Kasuwar Kurmi

  0
  1378

  Jabiru Hassan, Daga Kano

  AKALLA shaguna 30 ne suka kone a kasuwar Kurmi da ke Birnin Kano sanadiyyar wata gobara da ta tashi  a daren Larabar nan, kafin jami\’an kashe gobara da sauran al\’umma su murkushe wutar.

  Wakilinmu wanda ya ziyarci kasuwar da safiyar ranar Laraba, ya ruwaito cewa wutar ta tashi ne da misalin karfe 10 da rabi na dare, inda aka yi ta sanar da al\’umma ta kafafen yada labarai na jihar  domin a kai dauki, kuma bayan an dauki wani dan lokaci sai aka ci karfin gobarar.

  Gaskiya Ta Fi Kwabo ta duba yadda wutar ta yi barna a kasuwar ta kurmi , kuma masu shaguna da dama  sun bayyana yawaitar tashin gobara  a kasuwanni a matsayin wata jarrabawa daga Ubangiji, tare da yin kira ga \’yan kasuwa da su rika fitar da hakkin Allah daga cikin dukiyoyinsu domin  ta haka ne kadai za a sami tausayawa daga Allah, sannan Ya ba mu zaman lafiya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here