Jami\’an Tsaro Sun Kamo Shanu 750,Tumaki 320 A Buruku

0
1137

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

RUNDUNAR jami\’an tsaro ta Operation Yaki a Jihar Kaduna ta samu nasarar kamo shanu 750 Tumaki 320 daga dajin Buruku a hanyar Birnin Gwari.

Shugaban rundunar na Jihar Kaduna Kanar Yusuf Yakubu Soja ne ya shaida wa manema labarai hakan a Kaduna.

Inda ya tabbatar da cewa wannan koakari ne da suka saba yi tun da Dade wa a kokarin ganin an tsarkake jihar daga masu aikin satar shanu da sauran ayyukan batagari.

\”Don haka muna kira ga daukacin jama\’a ga duk Wanda ya San an sace masa Dabbobi da lallai yazo Kaduna domin tafiya da shanunsa ko Tumaki\”.

Su dai wadannan dabbobi wakilinmu ya yi tozali da su a cikin garin Kaduna inda aka biyo da su kan Titin Ahmadu Bello cikin garin Kaduna a bainar jama\’a har suna ta daukar hotunansu suna kuma jinjinawa jami\’an tsaron da suka yi wannan aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here