Rabo Haladu Daga Kaduna
Hukumar da ke yaki da yi wa tattalin
arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kwace
gwala-gwalan da darajarsu ta kai miliyoyin
naira daga hannun tsohuwar ministar mai,
Diezani Alison Madueke da kuma matar
wani makusancin tsohon shugaba Goodluck
Jonathan.
Mai magana da yawun hukumar, Wilson
Uwujaren wanda ya tabbatar wa da manema
labarai ce wa yanzu haka hukumar na cigaba da
bincike a kan tsohuwar ministar.
Sai dai bai bayyana darajar gwala-gwalan da
EFCC ta kwace ba, ko da yake wata kafar watsa
labarai ta ce darajar gwala-gwalan da
kuma wani agogon hannu ya kai fiya da naira
miliyan 593.
A baya-bayan nan ne dai hukumar binciken
manyan laifuka ta Birtaniya NCA ta gudanar da
wani bincike a kan Diezani Alison-Madueke
A shekarar 2014 ne kuma tsohon shugaban
babban bankin kasa Sanusi Lamido Sanusi, ya
zargi babban kamfanin man fetur
wanda Diezani ke shugabanta, da kin saka $20
biliyan a lalitar gwamnatin tarayya kamar
yadda dokar kasa ta tanada.
Shugaban Muhammadu Buhari ya ce
gwamnatinsa za ta yaki cin hanci da rashawa
musamman a bangaren man fetur