Rabo Haladu Daga Kaduna
HUKUMAR da ke yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kwace
gwala-gwalan da darajarsu ta kai miliyoyin naira daga hannun tsohuwar ministar mai,
Diezani Alison Madueke da kuma matar wani makusancin tsohon shugaban kasa, Goodluck
Jonathan.
Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren wanda ya tabbatar wa da manema
labarai cewa yanzu haka hukumar na ci gaba da bincike a kan tsohuwar ministar.
Sai dai bai bayyana darajar gwala-gwalan da EFCC ta kwace ba, kodayake wata kafar watsa
labarai ta ce darajar gwala-gwalan da kuma wani agogon hannu ya kai fiya da naira miliyan 593.
A baya-bayan nan ne dai hukumar binciken manyan laifuka ta Birtaniya NCA ta gudanar da
wani bincike a kan Diezani Alison-Madueke
A shekarar 2014 ne kuma tsohon shugaban babban bankin kasa Sanusi Lamido Sanusi, ya
zargi babban kamfanin man fetur wanda Diezani ke shugabanta, da kin saka Dala Biliyan ashirin ($20) a lalitar gwamnatin tarayya kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Shugaban Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yaki cin hanci da rashawa
musamman a bangaren man fetur