Rabewar Shi\’a Gida Biyu A Najeriya

0
1368

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

A wani al\’amarin da ya bayyana a fili tsakanin mabiya kungiyar Shi\’a a tarayyar Najeriya na nuni da cewa a halin yanzu kungiyar ta dare gida biyu.

Hakan kuwa ya fito fili ne tun bayan da wani bangare mai suna cibiyar Rasulull A\’azam suka yi wani babban taron tattaunawa da jami\’an tsaro a Kano.

Wani jigo a cikinkungiyar mai suna Shaikh Sale Zariya ya bayyana cewa mafi yawan wasu da suke ikirarin su mabiya Shi\’a ne ba su san me ake kira shi\’a ba don haka ake samun matsala a wadansu lokuta.

A Cesar shugabansu cibiyar Rasulull A\’azam Malam Nura Dass, ya tabbatar da cewa su malamansu sun yi masu umarnin bin doka da oda, musamman wajen yin Hulda da gwamnati ba kamar yadda wasu suke daukar lamarin ba sai an bijirewa hukuma,lallai wannan ba karantarwar Shi\’a ba ne don haka ba su goyon bayan bijirewa duk wata hukuma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here