Rabo Haladu Daga Kaduna
SHUGABANNIN Fulani a Najeriya sun ce wasu mutane ne ke yin sojan-gona suna
aikata laifuka sannan su dora alhakin hakan kan \’ya\’yan Fulani.
Shugabannin sun yi wannan bayani ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zargin Fulani
makiyaya game da hannu a aikata miyagun laifuffuka kamar kai hare-hare da fashi da
makami da fyade.
Sarkin Fulani na shiyyoyin kudu-maso-gabas da kudu-maso-kudancin Najeriya, Ardo Sa\’idu
Baso, ya shaida wa manema labarai cewa kodayake a wasu lokutan Fulani na aikata laifuka, amma
yawancin lokuta ba su ne ke aikatawa ba.
A cewarsa, \”Ba ma jin dadin yadda ake danganta duk wani ta\’addanci da \’yan
Fulani. Akasari mu ake cutarwa.Wani lokaci idan mun yi bincike muna gano cewa ba \’yan
Fulani ne ke aikata miyagun laifukan ba\”. Ardo Sa\’idu Baso ya amince cewa akwai bata-
gari a cikin Fulani, yana mai yin kira a gare su da su daina aikata laifuka.