Daga Usman Nasidi
A ranar Juma’ar da ta gabata ne al’ummar Unguwar Ja’en a yankin karamar Hukumar Gwale cikin Jihar Kano suka samu kansu cikin alhini a sakamakon gano gawarwakin yara kanana guda hudu da suka yi a cikin wata mota a wani kango da ke unguwar.
Rahotanni sun bayyana cewa yaran wadanda dukkansu ‘yan unguwar ne, wato Alkashim Shehu Magashi da Mahboob Surajo da Umar
Surajo da Shahid Auwal, sun shafe sama da awanni biyar a cikin motar kafin daga bisani a iya gano gawarwakisnu a cikin wannan motar.
Alhaji Shehu Magashi shi ne mahaifin Alkasim dan kimanin shekaru uku da haihuwa, ya bayyana cewa yaran sun mutu ne a sakamkon
rashin iska a cikin motar, kasancewar duk tagogin motar a rufe suke lokacin da suka shiga,
Haka kuma yaran saboda shekarunsu ba su iya sauke gilashin motar ba,haka kuma ba su iya bude kofar motar ba. “Lokacin da muka isa wurin sai muka tarar da gawarwakin yaran kwance a cikin motar, da ka gansu ka san sun yi kuka sun gaji kafin su rasu, sai dai kasancewar gilasan motar a rufe suke babu wanda ya iya jin su ballantana ya taimaka masu.”
Binciken da wakilinmu ya yi ya gano cewa tun misalin karfe 12:00 na ranar Juma’ar ne iyayen yaran wadanda makwabtan juna ne suka nemi yaran, wadanda dukkaninsu shekarunsu ba su wuce shida ba, suka rasa, hakan ya sa suka bazama neman yaran ba tare da sanin yaran suna cikin motar da ke ajiye a cikin kangon da ke makwabtaka da gidajensu ba.
Malama Fatima Surajo ita ce mahaifiyar Mahboob surajo da Umar surajo, ta bayyana cewa, lokacin da ba ta ga yaranta ba ta yi zaton
suna makwabta ne, har sai da ta ga an dauki tsawon kusan awa guda ba su shigo ba sannan ta fara nemansu.
Ta ce “Da farko da ban gansu ba na yi zaton gidan makwabta suka shiga don yin wasa, da ba mu ji duriyarsu ba sai muka tafi yawon nemansu, muna kan hanyar dawowa ne muka tarar an gano gawawakinsu a cikin mota. Ina yi masu addu’ar Allah Ya jikansu.” Ta karasa cikin kuka.
Ita ma mahaifiyar Shahid Auwal, Malama Aisha Auwal, ta bayyana cewa tsautsayi ne ya sa dan nata ya fita, domin kodayaushe gidansu yana kulle ne.
Ta ce “Allah Ya sanya hakan ne hanyarsu, tsautsayi ne. A kullum kofar gidan nan a rufe take, ban san cewa da na yi baki aka bude gidan shi kuma ya yi amfani da wanann damar ya fita ba. Sai bayan dan lokaci kadan sai na lura cewa ba ya gida. Nan da nan na neme shi, inda kuma ba mu gan shi ba sai dai gawarsa.” Inji ta.
Alhaji Ahmad Abdulalhi Yakasai shi ne mai motar da aka tsinci gawarwakin yaran a ciki, ya bayyana wa Gaskiya Ta Fi Kwabo cewa ya ga gawarwakin yaran ne a daidai lokacin da yake kokarin mayar da batirin motarsa wanda ya kai shi caji.
Ya ce “A ranar Laraba na cire batirin motar na kai shi unguwar Saharada inda aka yi min cajinsa. To a ranar Juma’ar ne a kan hanyata ta dawowa gida sai na tsaya na karbo batir din, don haka da na dawo ko gida ban shiga ba sai na kira matata na ce ta kawo min mabudin motar.
Da ta kawo min mabudin ne take gaya min labarin batan yaran. Lokacin da nake kokarin bude motar ne sai kawia na yi arba da gawarwakin yaran a cikin motar.” Inji shi.