Za Mu Kawo Karshen Ayyukan Ta\’addanci A Kaduna – El-Rufa\’i

0
1034

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN Jihar Kaduna ta ce tana kokarin ganin al\’amura sun daidaita ta fuskar tsaro
bayan da a kwanan nan aka yi ta samun matsalar garkuwa da jama\’a don neman
kudin fansa da kuma barayin shanu.
Gwamnatin jihar ta raba wa jami\’an tsaro babura domin inganta sintiri, ta kuma ce
kokarinta shi ne ganin bayan barayin shanun da suka koma sace jama\’a don neman kudin
fansa.
An dai raba wa jami\’an tsaro da suka hada da \’yan sanda da sojoji da jami\’an kare aukuwar
hadura ta kasa wato FRSC babura 51 don yin wannan aiki.
Gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufa\’i ya ce, \”In sha Allahu nan ba da dadewa ba za mu
kawo karshen irin wadannan ayyukan ta\’addanci a Jihar Kaduna da kewaye.\”
Yawanci maharan na aikata ayyukansu ne a dazukan Birni-Gwari inda nan maboyarsu take.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here