ZUWA ga Edita: Bayan gaisuwa mai yawa gare ka da sauran abokn aikinka, ina son ka ba ni fili a wannan jarida mai albarka in ce wani abu.
Da farko dai ina mai jinjina wa \”yan majalisun tarayya, bisa hadin kan da kuka samu a tsakanin ku domin mun jima bamuji labarin an ba wa hammata iska ba.
Bayan haka ina so na yi kakkausar suka dangane da wasu \’kudurori da manufofi da kuke aiwatarwa a majalisun naku, wanda a fili yake sun saba da muradun talakawanku da kuma na shugaba Baba Buhari.
Idan na fara da \’yan majalisar dattijai, a fili yake ba ku tausayin halin da kasarku take ciki da kuma halin da talakawan kasar nan suke ciki. Don haka nake shaida muku cewa zan ci gaba da wannan wasikar tawa a shirye-shirye na gaba.
Na gode. Naku Malal Kazeem
Karamar Hukumar Gamawa.